
Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA ta bayyana cewa har yanzu tana nan kan bakanta dake cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sabawa doka dakatarwar da yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.
Shugaban kungiyar, Afam Osigwe ne ya bayyana haka a wata hitmra da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Ya bayyana cewa, suna kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya dawo da Gwamna Simi Fubara akan mukaminsa.
Yace gwamnan rikon kwarya da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada ba bisa doka aka nadashi ba dan haka su basu yadda dashi ba.