Hezbollah ta harba gomman rokoki zuwa kudancin Isra’ila, a cewar ƙungiyar a wata sanarwa.
Ta ce ta far wa shingayen sojoji da kuma wuraren ajiye makamai ta hanyar amfani da makamai masu linzami,a wani matsayin martani ga hare-haren da Isra’ilar ta kai kudancin ƙasar.
A wata sanarwa ta daban, dakarun tsaron Isra’ila (IDF), sun ce an harba rokoki aƙalla 35 daga Lebanon kuma hakan ya shafi shingayensu.
An jikkata wani mutum mai shekara 50 a yankin Galilee, a cewar sojoji Isra’ila.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojin saman ƙasar sun kakkaɓo rokoki da dama da Hezbollah ɗin ta harba yayin da wasu kuma suka yi lahani a wasu yankuna kusa da garin Ami’ad.