Tuesday, May 6
Shadow

Hoto: Karuwa ta kàshè abokin làlàtàrtà bayan da ya dauke ta ya kai gidansa

Wata karuwa ta kashe abokin lalatarta bayan da ya dauketa ya kai gidansa.

Lamarin ya farune a jihar Legas a unguwar Jakande.

Mutumin me suna Okafor ya dauki karuwar, Joy Kelvin ya kai gidansa inda a canne ta caka masa wuka ya mutu.

Lamarin ya faru a daren 6 ga watan October inda a wayewar gari watau ranar 7 ga wata sai abokin mamacin ya kira ‘yansanda.

An garzaya da Okafor zuwa Asibitin Marina inda a canne suka tabbatar ya mutu.

Tuni dai aka kama Joy inda shi kuma aka kai gawarsa zuwa mutuware yayin da aka ci gaba da neman ‘yan uwansa.

Karanta Wannan  Rabon da a ga tashin hankali irin wanda ya faru a shekarar 2023 tun yakin Duniya na 2

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *