Tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff ya kaiwa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyara a gidansa na Daura.
Ziyarar Modu Sheriff na zuwane bayan ta Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai data tsohon mataimakin shugaban kasa,Atiku Abubakar.
An fara rade-radin cewa, watakila wata hadakar siyasa ce take janyo wannan ziyarar.
Atiku Abubakar kuma ya kaiwa tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ziyara.