Hukumomin soji dana CJTF a jihar Borno sun kama wani soja da laifin satar harsasai.
An kama sojan ne me suna Corporal Francis Bako a tashar motar Kano dake Maiduguri.
An kamashi ne bayan samun bayanan sirri akan satar harsasan da yayi.
Sojan dai na kan hanyar zuwa Kadunane bayan da aka kamashi da harsasan guda 602 kuma yana tsare yanzu haka.