Babban Attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya kaddamar da kamfanin hada manyan Motoci a Legas.
Gwamnan Legas, Sonwo Olu, Kakakin majalisar tarayya, Goodswill Akpabio, na daga cikin wanda suka halarci bikin kaddamar da kamfanin.
kamfanin zai rika hada manyan motoci akalla dubu 10 a shekara kuma zai samarwa da mutane dubu 3 aikin yi.