Kasar Yahudawan Israela sun jefawa kasar Lebanon Rokoki 300 a wani sashi na ci gaba da yakin da suke da kungiyar Hezbollah.
Kasar ta Israela dai a cewarta ta gargadi fararen hula dasu tashi daga kusa da gidajen ‘yan kungiyar Hezbollah kamin su kai hare-haren.
Kasar tace ta gano ‘yan Kungiyar Hezbollah dake shirin kai mata hare-haren Rokoki shine ta dakile su.