Sunday, March 16
Shadow

Hukumar ‘yansandan Najeriya zata hukunta ‘yansanda masu cin zalin Direbobi suna karbar musu kudi a jihohin Inyamurai

Hukumar ‘yansandan Najeriya zata hukunta ‘yansanda da aka samu da cin zalin direbobi ta hanyar karbar musu kudi a yankunan jihohin Inyamurai.

Shugaban hukumar ‘yansanda ta PSC, DIG Hashimu Argungu rtd ne ya bayyana hakan inda yace ba zasu yadda da take hakkin bil’ada da ake zargin ‘yansandan da aikatawa ba.

DIG Hashimu Argungu rtd yace zasu fara aiwatar da hukuncin da aka tanadar akan irin wannan laifi na korar duk dansandan da aka samu da aikata laifin.

Argungu yayi maganane a wajan taron da ake yi akan lamarin tsaro da kare hakkin bil’adama a jihar Enugu.

Argungu wanda Mr. Ikechukwu Ani ya wakilceshi yace sun jima suna gargadin ‘yansanda da su daina aikata irin wannan laifi amma sun kiya.

Karanta Wannan  Gobarar Amerika: Yawan wadanda suka mutu sun karu a yayin da mahaukaciya Gobarar ke ci gaba da yaduwa

Yace dan haka zasu fara daukar mataki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *