Friday, January 16
Shadow

Hukumar zabe me zaman Kanta, INEC zata ci gaba da yiwa ‘yan Najeriya rijistar katin zabe

Hukumar zabe me zaman kanta tace zata ci gaba da rijistar masu zabe a ranar 17 ga watan Yuli a jihar Anambra inda kuma za’a ci gaba da yi a gaba dayan Najeriya a ranar 18 ga watan Augusta.

Shugaban hukumar, Prof. Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da aka yi ranar Alhamis a Abuja.

Ya bayyana cewa, za’a fara rijistar ne a jihar Anambra saboda zaben gwamna da za’a gudanar a jihar.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu yayi ikirarin cewa a lokacin da ya hau mulki Ana sayen dalar Amurka akan Naira 1,900 Saidai dai da yawa sun musanta wannan ikirarin na shugaban kasar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *