Thursday, December 25
Shadow

Idan Kun saci kudin Talakawa ku daina kaiwa kasashen Turawa>>Dangote ya baiwa barayin Gwamnati a Najeriya shawara

Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa bai kamata ace masu satar kudin talakawa suna kai kudaden kasashen turawa ba.

Dangote yace babu kasar da ba’a sata, amma banbancin misalin kasashen Asia dana Afrika shine, idan sun saci kudin suna zuba jari dasu ne a kasashen su maimakon kaiwa kasashen Turawa.

Dangote yace ba wai yana karfafawa jami’an gwamnati satar kudin talakawa bane amma yana da kyau su san cewa kamata yayi su rika amfani da kudin a cikin gida maimakon kaiwa kasar waje dan ci gaban kasar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda yaro tya shake Abokinsa saboda yace masa yana kama da shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *