Friday, October 4
Shadow

ILMI KOGI: Za Mu Iya Sàìťawa Mutum Kaddara Mai Kyau Tare Ďa Ķýawàwàɲ Dabi’u Tun Kafin Samun Cikinsa Zuwa Ya Zo Duniya, Inji Imam Assufiyyu

Imam Habibi Abdallah Assufiyyu, shahararren Malami kuma Shugaban Kungiyar Malamai Masana Ilimin Taurari Na Kasa (FANIS) ya ce “Muna iya śàìțàwa wanda ba a haifa ba kýaķķýawan kaddara da dabi’u masu inganci tun kafin a samu cikin sa zuwa a haife shi ya zo duniya, a karshe kuma ya samu muwafaka mai girma a rayuwa. Saboda haka wannan al’amari ne da iyaye ya kamata su maida hankali akai domin samarwa ‘ya’yan su kyakkyawar gobe.

Shehin Malamin ya kara da cewa “Kuma a shirye muke domin taimaka ma dukkan wanda yake son ya ga haka ta faru ga rayuwar ‘ya’yansa, wanda zai sa su samu sauki wajen tarbiyar ‘yantar da su a rayuwa”.

Ta hanyar amfani da Ilimin Falaki dan Adam zai samu ingantacciyar rayuwa mai cike da tsari da manyan nasarori wadanda tunani ko hankali bazai iya hikayo su ba, batare da jingina ga doron ilimi ba”.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Shugaba Tinubu zai gabatar wa majalisa kudirin dokar kwarmata bayanai ba da jimawa ba - Ministan kudi Wale Edun

Me za ku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *