Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince da cewa ya yadda ana shan wahala a Najeriya.
Tinubu ya bayyana hakane a ganawar da yayi da tsaffin shuwagabannin majalisar tarayya wanda Ken Nnamani ya jagoranta.
Ya bayyana cewa sakacin gwamnatocin da suka gabata ne ya jefa kasar a halin da take ciki.
Yace amma da hadin kai da aiki tare za’a samu ci gaba a Najeriya.
Tun bayan da shuyaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya cire tallafin man fetur ne dai Najeriya ta shiga cikin halin matsin tattalin arziki wanda har yanzu bata fita ba.