Thursday, October 3
Shadow

Taron Barayine a cikin gwamnatin Najeriya ta yanzu dan haka kada kuyi tsammanin su kawo muku gyara>>Inji Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasa,Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, barawo wanda ya saba rashawa da cin hanci ba zai taba kawo ci gaban kasa ba.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.

Obasanjo yace akwai wasu cikin bangaren zartaswa da wasu cikin bangaren majalisa da barayi ne ya kamata ace suna daure a gidan yari.

Yace wasu ‘yan siyasa sun mayar da siyasa a matsayin wuri wanda ba da’a ba sanin ya kamata,yace akwai dan siyasar da ya bashi mamaki saboda ya halasta satar dukiyar jama’a.

Sannan akwai wani shima wanda suna taro yayi karya,bayan da aka kammala taron ya tambayeshi me yasa yayi hakan,sai yace masa ranka ya dade ai siyasa kenan.

Karanta Wannan  Hotuna: 'Yan Bindiga sun kashe babban soja da bai dade da yin aure ba da sauran sojoji 3 a Sokoto

Yace wasu kawai sun mayar da siyasa wurin da ba sa’a ba sanin ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *