Friday, February 13
Shadow

Ina son shiga Aljannah>>Inji Shugaban kasar Amurka, Donald Trump

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana son shiga Aljannah.

Ya bayyana cewa dalili ma kenan da yake ta kokarin ganin ya kawo karshen yakin kasashen Russia da Ukraine.

A baya Shugaba Trump ya gana da shugaban kasar Russia, Vladimir Putin sannan ya gana da shugaban kasar Ukràìnè sa shuwagabannin kasashen Turai.

A nan gaba yace zai hada Putin da Zelenskyy su yi zaman sulhu.

Tun kamin ya zama shugaban kasa yayi Alkawarin cewa idan ya ci zabe, zai tabbatar ya kawo karshen yakin.

Karanta Wannan  Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace zai fara baiwa 'yan Cirani da basu da takardu Dala Dubu daya kyauta kowannensu dan su fice su koma kasashensu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *