Tuesday, March 17
Shadow

Inna Lillahi wa inna ilaihi raji’un: Malamin jami’a ya rigamu gidan gaskiya a dakin Daliba bayan da ya kai mata ziyara

Wani Malamin jami’a me suna Abdulfatai Aiyede ya rigamu gidan gaskiya a dakin daliba bayan da ya kai mata ziyara.

Malamin me shekaru 53 ya fito ne daga garin Bida inda ya kaiwa dalibar me suna Stella Joseph ‘yar kimanin shekaru 23 ziyara a Minna.

Dalibar tana karatun Nurse ne inda bayan da ya je dakin nata, ta dafa masa abinci.

Bayan da ya ci abincinne sai ya yanke jiki ya fadi yana jijjiga, an garzaya dashi Asibiti inda likitoci suka tabbatar ya rasu.

An kama dalibar inda shi kuma ake binciken gawarsa dan tabbatar da sanadiyyar mutuwarsa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Ku a ganinku dadi Muke ji a matsayin mu na Gwamnoni koh, Toh wahala muke sha>>Inji Gwamnan Katsina Dikko Radda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *