Thursday, February 26
Shadow

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Ji abinda wasu da ba musulmai ba suka yi a babban masallacin Manchester dake kasar Ingila ana tsaka da sallar Tarawihi

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar 24 ga watan Fabrairu, wasu mutane 2 wanda ba musulmai ba sun shiga babban masallacin Manchester dake kasar Ingila yayin da ake tsaka da sallar Tarawih.

Masallatan sun kama daya da wasu maqamay a hannunsa an bayyana mutumin a matsayin dan kimanin shekaru 40 inda kuma dayan ya tsere har yanzu ana nemansa.

Babu dai rahoton cewa, wani ya jikkata ko rasa rai.

Firaiministan Ingila, Keir Stermer yayi Allah wadai da lamarin inda ya jinjinawa wadanda suka kama daya daga cikin masu laifin.

Ya bayyana cewa sun ware kudi har fan Miliyan £40 dan samar da karin tsaro a masallatai da makarantun Islamiya, da kuma yankunan da musulmai suke.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Dan uwan Kwankwaso na jini, Yahya Musa Kwankwaso ya watsar da NNPP inda yabi Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC

Rahotanni sun ce masallacin ya dauki matakan tsaro dan kiyaye kara faruwar hakan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *