Iyalan Mafarautan Da Aka Kashe A Edo Sun Yi Zanga-zangar Neman Diyya.

Iyalan wasu mafarauta da suka rasa rayukansu a harin da ya faru a jihar Edo sun gudanar da zanga-zanga domin neman a biya su diyyar ‘yan uwansu da kuma gurfanar da wadanda suka aikata wannan mummunan laifi.
Zanga-zangar, wadda ta gudana kwanaki 40 bayan aukuwar lamarin, ta samu halartar daruruwan ‘yan uwa da abokan arziki na wadanda abin ya shafa, wadanda suka fito dauke da takardu da hotunan wadanda suka mutu suna rokon gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa.
Wani daga cikin shugabannin iyalan, ya bayyana cewa:
“Har yanzu ba a kama ko daya daga cikin wadanda suka aikata wannan kisa ba. Mun gaji da jiran shiru. Muna so a tabbatar mana da adalci kuma a tallafa mana da diyya domin wadanda suka bar iyali da yara.”
Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar Edo da su shiga cikin lamarin don tabbatar da adalci da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman a yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga ko wasu ‘yan ta’adda.
Gwamnatin jihar Edo dai ba ta fitar da wata sanarwa ba a hukumance game da wannan zanga-zanga, sai dai jami’an tsaro sun tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin.
Wannan zanga-zanga na zuwa ne yayin da jama’a ke kara bayyana damuwa kan yadda rashin hukunta masu laifi ke kara dagula zaman lafiya a sassan kasar.