Wednesday, January 15
Shadow

‘Jami’an tsaro shida na cikin mutanen da aka kashe a harin Katsina’

Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Katsina ta ce akwai dakarunta huɗu da kuma dakarun tsaro biyu na gwamnatin jihar cikin mutanen da ‘yanbindiga suka kashe a harin da suka kai ranar Lahadi.

Kakakin ‘yansadan a Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa an tsaurara tsaro a yankin ƙaramar hukumar Kankara, inda suke aiki da sauran hukumomin tsaro don kare sake aukuwar harin.

“A ranar 8 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 3:00 na rana maharan suka far wa garuruwan Gidan Tofa da Dan Nakwabo, inda suka harbe mutum 20 tare da raunata wasu biyu, sannan suka yi wa motarmu mai silke kwanton ɓauna kuma suka kashe jami’an ‘yansanda huɗu da kuma biyu cikin dakarun tsaron gwamnatin Katsina (KSCWC),” in ji sanarwar.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Tinubu Ya Aika Da Ƙudirin Biyan Mafi Karancin Albashi na Dubu N70,000 Ga NASS

Tun da farko rahotonni sun ce aƙalla mutum 25 aka kashe a hare-haren sannan aka sace wasu da ba a san adadinsu ba.

An yi jana’izar wasu daga cikin mutanen da aka kashe yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da laluba dazukan da ke kusa don ƙwato waɗanda aka sace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *