
Jam’iyyar adawa ta LP a Najeriya ta nesanta kanta daga shiga kowace irin ƙawance dmin tunkarar zaɓen 2027.
Kwamitin zartarwar jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ne ta tababtar da haka lokacin wani taro da ta gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar.
A baya-bayan nan dai jam’iyyun hamayya a Najeriya na ta ƙoƙarin ƙulla wata haɗaka domin tunkarar jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
To sai dai jam’iyyar ta LP ta ce ba za ta shiga kowace irin haɗaka.
“Taronmu a jajjada cewa jam’iyyarmu ba ta ciki, kuma ba za ta shiga kowane irin haɗaka ba domin tunkarar zaɓen 2027, a maimakon haka jam’iyyar LP za ta mayar da hankali wajen sake gina kanta ta hanyar ɓullo da sabbin sadaru da ƙarfafa kanta domin samun nasara a zaɓen 2027”, in ji Abure.