
Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana goyon baya ga Kwankwaso a bayyane a yayin da Gwamna, Abba Kabir Yusuf ke shirin komawa APC.
An ga Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a gidan Kwankwaso ranar Laraba a yayin da wasu ‘yan kwankwasiyyar suka kaiwa Kwankwaso ziyara a gidansa dake Kano.
Ya zauna a kusa da Kwankwaso yayin ganawar wanda da yawa ‘yan Kwankwasiyya suka bayyana cewa hakan alamar nuna yana tare da Kwankwaso ne.