‘Yan Bindiga a babban birnin jihar Naija watau Minna sun shiga wani rukunin gidaje me suna M.I Wushishi Estate inda suka lalata ababen hawa sannan suka yi gargadin a tashi daga gidan ko kuma idan suka dawo zasu kashe duk wanda suka iske.
Wani shaidan gani da ido yace lamarin ya farune da rana tsaka.
Yace maharan sun shiga rukunin gidajenne yayin da mazajen gidan ke wuraren aiki.
Kakakin ‘Yansandan jihar, Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace amma yanzu kura ta lafa.