
Hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya, NAPTIP tace matasan jihar Anambra sun baci da dabi’ar sayar da jarirai.
Kwamandar hukumar ta jihar, Ibadin Judith-Chukwu ce ta bayyana hakana wata sanarwa data fitar inda tace abin yayi yawa tsakanin matasa.
Tace abin yafi kamari a kauyuka dan hakane suka kafa wata tawaga ta musamman dan yaki da wannan mummunar dabi’a.
Ibadin Judith-Chukwu tace matashi zai yiwa yarinya ciki dai ya aureta amma tana haihuwar jaririn sai ya lalaba ya saceshi ya sayar bada sanin mahaifiyar ba.
Tace amma suna ta kokarin wayarwa da mutane kai game da lamarin.