Monday, April 6
Shadow

Jigo a Jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi yace a shirye yake ya koma APC duk da a baya ya soki jam’iyyar

Jigo a jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi ya bayyana cewa, a Shirye yake ya koma jam’iyyar APC duk da a baya ya soki jam’iyyar da salon mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.

Yace lallai a baya ya soki Gwamnatin Tinubu amma a yanzu idan dai ya samu dama, zai iya komawa jam’iyyar APC.

Yace kuma a shirye yake dan yin aiki tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu din domin ko da a baya dama yayi aiki tare dashi.

Karanta Wannan  Sharudan da aka gindaya min kamin a mayar da ni Gwamna basu da dadi amma na amince>>Inji Fubara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *