Thursday, February 5
Shadow

Jihohin Taraba, Adamawa, Borno da Yobe sun fada duhu bayan da wutar Lantarkinsu ta lalace, ji ranar da za’a gyara

Jihohi 4 daga cikin 6 na yankin Arewa maso gabas, watau jihohin Taraba, Adamawa, Borno da Yobe sun fada duhu bayan da wutar lantarkinsu ta lalace.

Da misalin karfe 10:00 am na safiyar ranar Talata, 10 ga watan Yuni ne wutar ta samu matsala. Kuma ana tsammanin sai nan da Ranar Asabar, da misalin karfe 5:00 pm za’a gyara wutar.

Lamarin ya taba harkokin kasuwanci a jihar inda dama saidai su koma amfani da janareta, ko Sola wanda kuma basu da wannan saidai su hakura.

Kamfanin Yola Electricity Distribution Company, YEDC yace dauke wutar ya zama dole dan a inganta injinan ko yanayin samar da wutar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Mijin Matarnan da 'ya'yanta da aka wa aika-aika a Dorayi ya je fadar Sarkin Kano dan sarkin ya masa ta'aziyya

Kamfanin ya bayyana jin dadin hakurik mutane da hadin kan da suka bayar kan wannan aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *