
Wani Inyamuri me suna Chinonso ya yi kira ga jam’iyyar ADC cewa, kada su amince da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso inda yace yana zargin zai je jam’iyyar ne dan yawa Tinubu aiki.
Ya bayyana cewa shi ko fadan Kwankwaso da Abba yana ganin shiri ne kawai.
Jaridar Thisday tace ana tattaunawa tsakanin Kwankwaso da jam’iyyar ADC inda yake shirin komawa can yayin da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ke shirin komawa APC.
Hakanan shima a jawabinsa, Kwankwaso yace akwai jam’iyyar da suke tattaunawa da ita yake son komawa amma kuma yana son a bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa.
j