
Rahotanni daga jihar Yobe na cewa, wani mutum ya tsallaka katangar maqabartar Potiskum ya tone Qabarin wani jariri sannan ya tsere da gawar.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya koka da yawaitar tone-tonen Qaburbura a jihar.
Inda yace ko a farkon watannan sai da suka samu Rahoton irin hakan a Karamar hukumar Jakusko inda har yanzu suna neman wanda ake zargin.
Kwamishinan ‘yansandan jihar CP Emmanuel Ado ya yi Allah wadai da lamarin inda ya baiwa duk DPO dake fadin jihar umarnin su saka ido a maqabartun jihar dan hana irin haka faruwa.