Wednesday, January 15
Shadow

Kaikayin Azzakari

Kaikayin Azzakari na daya daga cikin matsalolin da maza kan yi fama dasu, a wannan bayanin, zamu fadi abubuwan dake kawoshi da kuma maganinshi.

Abubuwan dake kawo kaikayin Azzakari sune:

Infection: Idan ya zamana kana fama da infection akan azzakarinka ko a cikinsa, zaka rika iya yin fama da kaikayin Azzakari.

Ciwon fata ko bushewar fata: Idan ya zamana kana fama da yawan bushewar ko wata cuta a jikin fatarka, zaka iya yin fama da kaikayin Azzakari.

Cutukan da ake dauka a wajan jima’i: Idan ya zamana ka kamu da daya daga cikin cutukan da ake dauka a wajan jima’i zaka iya yin fama da kaikayin Azzakari.

Karanta Wannan  Sau nawa ake jima'i: Sau nawa ya kamata ayi jima'i

Sabulu da Ake amfani dashi: Kalar sabulun da ake amfani dashi wajan wanka zai iya kawo kaikayin Azzakari.

Aske Gashin Gaba: Aske gashin gaba na daya daga cikin abubuwan dake kawo kaikayin Azzakari.

Abubuwan dake maganin kaikayin Azzakari

Dan maganin kaikayin azzakari, a wanke wajan da ruwan dumi.

Ana kuma iya amfani da man shafawa na magani ko asha maganin na rage radadi.

Idan kaikayin bai daina ba, a tuntubi likita.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *