Wednesday, January 15
Shadow

Kalaman barkwanci a soyayya

Kece Tabarmar baccina.

Dan wake da mai da yaji na.

Ina sonki kamar dan mangwaro idan yazo karshe.

Soyayyarki ta fi min rake zaki.

Da fari nasha tsikarina aka yi ashe soyayyarki ce ta sokeni.

Soyayyarki ta hanani ganin kyawun sauran mata.

Ko idona a rufe zan iya kai kaina gidanku.

Ko da mota, jirgin sama, Keke da babur sun daina aiki, zan iya yin tattaki daga Maiduguri zuwa Legas dan kawai in ganki.

Kin sace komai na jikina kin maye su da soyayyarki.

Bani da labari sai naki ko da cikin abokai da ‘yan uwana.

Duk macen dana kalla, fuskarki kawai nake gani a jikinsu.

Kar ki jini shiru ni kaina na manta da kainane bayan zurfin da na yi a tunaninki.

Zan iya shan shayi ba madara ba suga, zan iya cin abinci ba yaji ba miya ko gishiri muddin kece zaki bani.

Karanta Wannan  Labarin soyayya

Zan iya zuwa ko ina a kafa ko da ban saka takalmi ba dan kawai in ganki.

Ranar nan kawai ji nayi na cire kunya ina rawa a cikin gidanmu gaban kowa bayan da naji wani mawaki yana yabon sunanki.

Ke nifa na zauce indai akanki ne.

Zaki jini wani lokaci ina magana kamar dolo ko dan kwaya, giyar sonki ce na kwankwada.

A garinnan ban ga me rabani dake ba ko da sarki ne, soja ko dansanda.

An taya soyayyar ki wai za’a siya dan in daina sonki, nace ai ba’a yi kudin da zasu sayeta ba.

KALAMAN SOYAYYA A TSAKANIN MA’AURATA

ℳa’aurata suna daukar duhun Kai ko in ce girman Kai a kan nuna wa junansu soyayya bayan AURE.

Wanda yana Daga cikin Babban gibin da auren yake samu.
Misali.
Ya kamata na miji ya dinga daurewa ko kakane yana nunawa matar sa soyayya.
Yana gaya Mata maganganun soyayya ❤ irin su.
INA SONKI
INA KAUNARKI
KE CE MACEN DA NAFI SO A DUNIYA
ko Kazan nan yayi miki kyau da dai sauran maganganun na nuna soyayya da kulawa.
Wanda haka zai sa taji itama ba ta da masoyi daya fi shi.
Kuma wannna kalmomin ba zasu taba bacewa ba a cikin kwakwalwarta.
Kuma zasu ta dinga yawan nishadi da jin ita Mai sa’a ce a rayuwar aurenta.

Karanta Wannan  Soyayya text message

AMMA DAN ALLAH KANA NUNA MATA IRIN HAKA A RAYUWAR AURE KU ?

DAN UWA KA GYARA KADA KA BARI TA DINGA JI A BAKI WASU HAKAN ZAI BATA DAMAR TSANA A RAYUWAR AURE KU.

HAKA idan mace ce take gayawa mijinta
Yar uwa soyayya bata tsufa a wanna rayuwa koda kina da shekara 80 kice masa.

yallabai Ina son ka.
dear I love you.
Kai ne mijin da kafi kowanne birge Ni.
ko ta ce ai Ni duk wani Abu da kake so Ina son shi.
ko in zai fita kice Allah ya dawo min da Kai lafiya.
❊ ko in yayi kwalliya kice kayi kyau fa darling.
Da sauran maganganun nuna soyayya da kambama shi kina nuna yafi kowa.

Karanta Wannan  Sakon soyayya na dare

Wannan zai sa ki kara soyuwa a zuciyarsa, ki zama ta gabab goshinsa, kullum ya dinga jin sonki da son kusantar ki, ya kuma tabbatar a ransa kin Riga kin sallama masa, sai shi ma ya sallama ki, Amma sabanin hakan yawancin ma’aurata sai
girman Kai.
kunya da Jan aji ya Hana su yin irin wannan al’amarin da yake rage shakuwa a tsakanin ma’aurata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *