Monday, December 16
Shadow

Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

Mahajjatan Najeriya a kasar Saudiyya sun koka da kalar abincin da ake basu duk da biyan Naira Miliyan 8 a matsayin kudin aikin hajjin bana.

Daya daga cikin mahajjatan me suna Babagana Digima ne ya wallafa hoton kalar abincin da ake basu a shafinsa na facebook.

Abincin dai koko ne da kosai guda 3.

Babagana Digima ya kara da cewa, mahajjata yanzu sun koma bara dan neman abinda zasu ci saboda kudinsu dala $300 daya rage daga cikin dala $500 da suke da ita har yanzu ba’a basu ba.

Hukumar Alhazai ta kasa, National Hajj Commission of Nigeria (Nahcon) da take martani akan lamarin, tace ta sa a yi bincike kan lamarin.

Karanta Wannan  Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar Ya Naɗa Babban Malamin Addinin Musulunci, Farfesa Mansur Sokoto Sarautar Danmasanin Daular Usmaniyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *