An Kama Akwatin Zaɓe Da Na’urar BVAS A Motar Jigon APC, Mustapha Salihu, A Zaben Ganye.

Wasu jami’an tsaro a jihar Adamawa sun gano akwatin zaɓe da na’urar tantance masu kada kuri’a (BVAS) a cikin motar Mustapha Salihu, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa (Arewa maso Gabas), yayin gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Ganye.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan siyasa da jama’a, inda ake zargin yunkuri ne na murde sakamakon zaɓe. An ce an kama kayan zaɓen ne yayin da ake gudanar da aikin tantance kuri’u a wasu rumfunan zaɓe, kuma hakan ya janyo tarin mutane da bacin rai.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro har yanzu ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, amma al’ummar yankin da dama na bukatar a gudanar da bincike tare da daukar mataki kan duk wanda aka samu da laifi.
Ana ci gaba da sa ido kan yadda zaben ke gudana tare da fargabar yiwuwar rikici idan ba a warware batun cikin gaggawa ba.