
Rahotanni sun tabbatar da cewa, a karshe, An samu wanda ya fito yace yana son Ummi Nuhu da gaske kuma zai aureta.
Daya daga cikin masu shirya fina-finan Hausa ne ya fito ya tabbatar da hakan.
Yace idan aka kammala komai, zasu sanar da jama’a hali da ake ciki.
Wasu dai na zargin wai kwadayin kudaden da aka tarawa Ummi ne ya kai mutumin wajanta.
Tun bayan hirar da Ummi Nuhu ta yi da Hadiza Gabon kuma aka tara mata kudi ake samun mutane na fitowa suna cewa suna sonta.