Thursday, December 25
Shadow

Kalli Bidiyo Da Duminsa: Tsorone yasa na ce zan auri ‘YarGuda, Na fasa, abokaina sun fara min dariya>>Inji Maiwushirya

Rahotanni da shafin Hutudole ke samu na cewa, Shahararren dan Tiktok, Idris Maiwushirya ya bayyana cewa ya fasa auren ‘YarGuda.

Ya bayyana hakane a wani Bidiyo daya wallafa a shafinsa na Tiktok wanda bayan kusan awa daya ya goge.

A cikin Bidiyon da wakilin hutudole ya kalla, Idris Maiwushirya yace tsoro ne yasa yace zai auri ‘YarGuda.

Yace ita kanta bata son auren inda yace ya yanke wannan shawara ne ba tare da sanin lauyoyinsa ba hakanan Abokai sun fara yi masa dariya.

Duk da cewa Maiwushirya ya goge wannan Bidiyon cikin sauri daga shafinsa, Kafar Hutudole ta samu Bidiyon,kuma muna kan Editin dinsa da mun kammala zamu dora muku shi a kasa ku ji ku gani da idanuwa da kunnuwanku abinda Maiwushirya yace.

Karanta Wannan  Jihar Gombe ta kulla yarjejeniya da kamfanin kasar China dan samarwa da kanta wutar Lantarki

Mun kammala Editing Video din.

Danna nan dan Kalli Bidiyon

A cikin Bidiyon dai, Idris Maiwushirya yace wani tsohon dan fim ne ya kaishi kara wanda bai san ko a baya ya taba masa laifi ba.

Rahotanni dai a baya sun ce, Idris Maiwushirya ne da kansa ya wallafa cewa, yana son auren ‘YarGuda kuma itama rahotanni suka tabbatar da ta amince.

Bayan hakanne kotu tace ba zata yanke musu hukunci ba tunda sun amince zasu yi aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *