
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da Umarni a jiharsa ta Borno cewa mutane su tashi da Azumi dan a roki Allah ya magance matsalar tsaro a jihar.
Gwamnan yace za’a tashi da Azuminne ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamba inda yace a hada da addu’o’i musamman saboda dawowar Kungiyar Bòkò Hàràm inda take ci gaba da kai hare-hare a jihar
Wannan na zuwane Kwanaki kadan bayan da Kungiyar ta Bòkò Hàràm ta Khashye Janar din Soja, Muhammad Uba.