Thursday, February 12
Shadow

Kalli Bidiyo: Idan kuna son kanku da arziki karku je wajan Likitan Hakori a Najeriya >>Inji Wani Bature bayan da aka masa aikin saka Hakori amma hakorin ya fadi a ranar

Wani Bature da akawa aikin saka hakori a Najeriya amma Hakorin ya fadi a ranar ya gargadi mutane kada su kai kansu wajan Likitan Hakori a Najeriya.

Ya bayyana cewa da farko ya je aka saka masa hakori inda yayi farin ciki sosai har ma ya sumbaci goshin likitan da ya masa aiki.

Saidai bayan da ya bar asibitin Hakorin, a ranar Hakorin ya fadi kasa.

Ya bayyana rashin jin dadinsa inda ya sake komawa Asibitin aka sake saka masa wani hakorin.

Saidai shima ya sake faduwa bayan kwanaki 3.

Dan haka ya hau shafinsa na sada zumuntaninda ya bayyana rashin jin dadi.

https://twitter.com/i/status/2021273136050622712
https://www.youtube.com/watch?v=MjEkAtjamVY?si=B05Fh6iax6R0P9xf
Karanta Wannan  Fadar Shugaban kasa ta karyata Rahoton dake cewa, Shugaba Tinubu zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *