
Babban malamin Addinin Musulunci a Jos, Dr. Musa Salihu Alburham ya bayyana cewa Sheikh Nura, Khalid, Watau Digital Imam ya mayar da Wiy Wiy kamar Shayi.
Ya kara da cewa, Kuma Malamin ya yiwa ‘yan mata da yawa fyade.
Ya bayyana hakane a yayin da yake bayar da taihin zaman Digital Imam Kansila da kuma binciken da aka yi akan Halayyarsa.
Hakanan daya daga cikin Yaran Malam Dr. Musa Salihu ya fito yace ‘ya’yan Digital Imam ko Hauka zasu yi ba kuka ba, sai an fadi halinsa tunda ba karya aka masa ba.
Tuni dai Sheikh Digital Imam ya fito ya mayar da raddi hakana kuma ‘ya’yansa ma sun mayar inda suke cewa ba zasu yadda ba sai sun shigar da kara.