
Hilda Baci data dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya a Legas ta rika bin mutane bakin titi tana raba musu shinkafar.
Hakan ya biyo bayan yawan da shinkafar ta yi duk da mutane kusan dubu 20 da rahotanni suka ce sun yi rijista dan zuwa wajan cin shinkafar
A baya dai an ga Bidiyon Hilda Baci na rokon mutane cewa su je su ci shinkafar dan ba yadda zata yi da ita, ta mata yawa.