
Wannan wani Bidiyo ne dake yawo a kafafen sda zumunta inda aka ga yanda wasu mutane suke ihun Kan Talakawa ya waye sannan suna fadar ADC a yayin da gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kai ziyara garin.
A Bidiyon dai an ga jami’an tsaro zagaye da tawagar motocin gwamnan yayin da mutane ke ta ifaceiface.
Babban dan Adawa na jihar Kaduna, Ashiru Kudan daga wanan gari na Kudan ya fito.
Hakana akwai takadda ma me zafi tsakanin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da gwamna me ci, Malam Uba Sani.