Dan majalisar kasar Faransa, Sébastien Delogu ya daga tutar Falas-dinawa a farfajiyar majalisar yayin da ake zaman zauren majalisar.
Dan majalisar yace kasarsa ta Faransa na da hannu a kisan kare dangin da Israela kewa Falas-dinawa ta hanyar sayarwa da Israelan makamai.
Yayi kira ga shugaban kasar, Emmanuel Macron da ya daina sayarwa da Israela makamai.
Saidai an dakatar dashi sannan aka bashi dakatarwar kwanaki 15.
Saidai bayan dakatar dashi, Dan majalisar ya shiga cikin masu zanga-zangar goyon bayan kasar ta Falas-dinawa a kan titi:
Saidai a wani lamari kuma na ban mamaki, shine, kakakin majalisar data dakatar dashi, itama an ganta sanye da tutar kasar Israela yayin da take wani jawabi.
Wannan yasa aka rika bayyana lamarin da son kai da munafurci.