
Fatima Hamza ta Izzar So wadda a baya ta fito tace wata alaka da bata bayyana ba ta shiga tsakaninta da jikan Sheikh Dahiru Usman Bauchi har ya cuceta ta saki sabon Bidiyo.
A sabon Bidiyon data saki an ji tana gyara maganar ta inda tace yaron ba jikan Dahiru Usman Bauchi bane, amma ita ya gaya mata cewa shi jikan Shehu ne.
Tace ta samu bayani kamar dan abokin malam ne.
Tace kuma ko me zai faru bata tsoro.
Hutudole ya lura cewa, ta goge tsohon Bidiyon data wallafa inda take cewa jikan Dahiru bauchine yaron.