
Tauraron mawakin Hausa, Musbahu M. Ahmad ya bayyana a wani bidiyo yana ihu yana fadar cewa Gwamnatin Kano zata yi jifar Gafiyar Baidu saboda komawar Gwamna Abba jam’iyyar APC.
Saidai wannan abu da yayi, ya dauki hankulan mutane inda wasu ke cewa, hakan bai kamata ba.
Wasu sun rika bayyana cewa, da sun dauki Musbahu me hankali amma yanzu ya fadi ba nauyi a wajansu.