
Bayan da tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya je ofishin jam’iyyar APC na jihar Gombe ya sabunta rijistarsa a matsayin dan jam’iyyar APC.
A wajan ya bayyana cewa tun shekarar 2001 yake a siyasa amma ba da rigar siyasa ba.
Saidai wani tsohon Bidiyon sa da yake wa’azi akan Munbari wanda rahotanni suka ce an daukeshi ne a shekarar 2008, Pantami yace shi ba dan siyasa bane.
Wannan tsohon Bidiyon da aka zakulo ya kawo muhawara da cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta.