Wednesday, April 8
Shadow

Kalli Bidiyon: Ba yaran nan kadai, har iyayensu ya kamata Shugaba Tinubu ya karramasu>>Inji Sheikh Gadon Kaya

Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Abdallah Gadon kaya yayi kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya karrama yara mata da suka yi nasarar lashe gasar Turanci ta Duniya tare da iyayensu.

Yace ya kamata a karrama hadda iyayensu saboda yanda suka kula dasu suka basu tarbiyya da ilimi da har suka kai wannan mataki.

Malam yace ba ‘yan kwallo kadai shugaban kasar zai rika karramawa ba.

inda yace shugaban zai bar mummunan tarihi idan bai karrama wadannan yara ba.

Wannan kira na malam na zuwane bayan na Sheikh Isa Ali Pantami na cewa ya kamata shugaba Tinubu yawa yaran irin karramawar da yawa ‘yan Kwallon Najeriya.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar da sojojin Najeriya 11 da kasar Burkina Faso ta tsare inda ya tabbatar da an sakesu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *