
Wani Bidiyo na Kwamishinan ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja yana cewa masu laifi da suke tsare dasu suna jin dadi ya dauki hankula.
An ganshi yana cewa, a dakin da suke tsare da masu laifin akwai na’urar sanyaya daki watau AC, sannan akwai Talabijin inda ake kallon gasar Premier League da labarai.
Saidai da yawa sun yi shakkun wannan ikirari nasa.