
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon wadda itace ta yi hira da Ummi Nuhu har lamarinta ya dauki hankula ta yi magana akan rahoton dake cewa ta baiwa Ummi tallafin Naira Miliyan 5.
Hadiza a Wani Bidiyo da aka ganta tare sa Ummi Nuhu tace ba Gaskiya bane, bata baiwa Ummi Nuhu Tallafin Naira Miliyan 5.
Saidai ta gabatar da Ummi ta yi jawabi da kanta:
Ummi ta tabbatar da samun tallafi daga mutane da yawa.