Thursday, August 6
Shadow

Magidanci a jihar Kaduna ya kai tsohuwar matarsa kotu saboda ta ki barin gidansa shekaru 2 bayan ya saketa

Wani magidanci a jihar Kaduna ya kai tsohuwar matarsa kotu saboda ta ki fita ta bar masa gida, Shekaru 2 bayan da ya saketa.

Mutumin wanda dan kasuwane me suna Dauda Dahiru ya kai tsohuwar matartasa karane kotun magajin gari dake Kaduna.

Da yake magana ta bakin lauyansa, Hassan Sadisu yace suna da ‘ya’ya 5 mata da matar tasa da yaro namiji 1.

Yace a lokacin da ya saketa tana dauke da cikinsa shine yace ta zauna sai ta haihu, yace amma ta haihu yanzu shekara 2 kenan da sakin amma taki fita daga gidan.

Yace ya ma sayar da gidan sannan yace zai kama mata wani gidan saboda yara amma taki yadda.

Karanta Wannan  Tinubu ya taya Donald Trump murna

Matar dai a nata martanin tace idan yana son ta tashi sai ya sai mata gida ko da me daki dayane ko kuma ya kama mata haya ya biya kudin haya na shekaru 5.

Saidai me shari’a, Mu’awiyah Shehu yace matar bata da hurumin sa tsohon mijinta ya mata wadannan abubuwa dan yanzu ba miji da mata ba suke.

Yace mata ‘ya’yansa ne kadai yanzu yake da hakkin kula dasu.

Alkalin ya daga shari’ar zuwa 8 ga watan Satumba inda yace matar ta nemo gida ylta kawowa kotu a sa mijin ya biya mata haya.

Saidai kotun ta kuma ce mata ta bar gidan tsohon mijin nata da take zaune nan take.

Karanta Wannan  Kotu taki amincewa da hana masu rike da mukaman siyasa zuwa kasashen waje neman magani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *