Tuesday, May 12
Shadow

Kalli Bidiyon: Kudi cike da Ghana Must Go ana rabawa mutane da hotunan Shugaba Tinubu akai da suka jawo cece-kuce

An ga Bidiyon kudi cike da jakar Ghana Must Go a Anbulan me dauke da suna da hoton shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ana rabawa mutane dan su sake zaben shugaban kasar.

Masu rabon kudin na sanye da riguna masu dauke da tamburan shugaba Tinubu kuma an jisu suna yarbanci.

Ko da a shekarar 2023 ma an ga irin wanan yanda aka rika rabawa mutane kudi a Ghana Must Go dan su zabi shugaban kasar.

A wancan lokacin har motar kudi irin ta banki aka ga ta shiga gidan na Tinubu dake Lagos.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a 6, da Litinin 9 ga watan Yuni, 2025 a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan babbar Sallah na bana

A wasu rahotannin daga baya bayan ya ci zabe, sun ce shugaba Tinubu ya rika bayyana cewa kudinsa suka bashi damar zama shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *