Friday, June 26
Shadow

Kalli Bidiyon: Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta shigarwa makarantar da ‘yata ta rasu, dan haka nima ina neman idan akwai kungiyar Musulmai nima su shigar min>>Inji Mahaifiyar Nihal

A jiyane dai muka kawo muku rahoton wata yarinya Nihal daga Kano wadda ta rasu a makarantar kwana.

Rahotannin farko sun bayyana cewa Gwale-gwale aka baiwa Nihal saboda bata yi sallah ba duk da ta gayawa malamin su cewa tana fama da rashin lafiya amma aka tilasta mata yin gwale-gwalen wanda shine yayi sanadiyyar mutuwarta.

Mahaifiyar Nihal a hirar da Freedom Radio suka yi da ita tace masu makarantar sun je gida suka mata gaisuwa suka ce mata wai diyarta bata da lafiyane shine aka mata addu’a a ruwa aka bata tasha daga nan ta rasu.

Tace amma sun gargadeta kada ta saurari duk wani labarin da za’a kawo mata.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda 'yan kasar Algeria ke ta murnar kaiwa ga Quarter finals, sun ce Sun gama da Dr. Congo saura Najeriya

Tace sun kaiwa ‘yansanda rahoto aka je makarantar dan zantawa da dalibai amma makarantar tace ba za’a zanta da daliban ba, inda suka iske Lauyoyi da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN.

Tace daga baya an je aka rubuta statement aka je aka shiga makarantar da karfi aka zanta da daliban.

Tace daliban sun gaya musu cewa, Nihal bata yi Sallah bane shine aka kamata za’a mata hukunci shine tace tana al’ada, ahine aka ce sai ta daga an gani, amma tace mamanta tace mata kada ta nunawa kowa jikinta.

Tace shine aka sakata kneels down a rana ta wuni a rana tana kuka tana cewa a bara ruwa tasha amma aka yi banza da ita har rai yayi halinsa.

Karanta Wannan  An yi zàngà-zàngàr neman a sauke shugaban INEC a Sokoto
@freedomradionigeria

Munyi imani da rasuwar ‘yata a makaranta saidai maganganun dake yawo tsakanin malamai da ɗalibai kan musabbabin rasuwarta shine abinda yafi damuna . Don haka muke neman hukuma ta shiga. -Mahaifiyar Nihal yarinyar da ake zargi ta rasu a makaranta a Kano.

♬ original sound – Freedom Radio Nigeria – Freedom Radio Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *