Friday, July 17
Shadow

Turawa sun ce wai dala Biliyan $38 na mallaka to ko Matatar man fetur dina kadai ta zarta dala Biliyan $40 kuma ina da kamfanoni da sauran kadarori da basu sakasu a lissafi ba>>Inji Dangote

A wata hira da aka yi dashi, Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, bayanin da turawa suke cewa wai kudinsa dala Biliyan $38 ne ba gaskiya bane.

Dangote yace ko matatar man fetur dinsa kawai ta fi Dala Biliyan $40.

Sannan kuma akwai wasu kadarorinsa da ba’a sakasu a lissafi ba.

Dangote da aka tambayeshi gashi yana da kudi amma baya alfahari sai yace tarbiyyar da ya samu daga gidane ba’a koya musu Alfahari ba.

https://twitter.com/i/status/2067288672043446613

Karanta Wannan  An zargi cewa An fifota baiwa Adam A. Zango kulawa fiye da sauran wadanda suka yi Hadari tare a Asibiti inda aka bar su duk da sun fi shi jin jiki, har daya ta rasu daga ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *