
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun taki sa’a da Allah ya basu shi a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar Katsina.
Da yake jawabi, Kashim Shettima yace Katsinawa sun yi dace da Allah ya basu Dikko Raddah a matsayin gwamnan, yace a tafa masa.
Sannan yace ‘yan Najeriya kuma sun yi dace da Allah ya basu shi a matsayin mataimakin shugaban kasa.