
Wani me shagon sayar da kayan sawa ya nuna bacin ransa sosai bayan da sabuwar ma’aikaciyar da ya dauka aiki ta samu kyautar Naira Dubu 60 daga wani da ya je shagon.
Yace satin ta biyu kacal da fara aiki a shagon kuma Albashin Naira dubu 50 yake biyanta.
A Bidiyon an ji kuma yana cewa, wani ma ya fara sai mata abinci.
Lamarin dai ya jawi muhawara kan aiki da irin wadannan abubuwan dakan dauke hankalin ma’aikata.